1. Duk lokacin da yaro ko yarinya suka kai matakin tashen balaga wato "early adolescence", musamman daga shekara 11, 12 zuwa 13... 18... To wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga yara da iyayensu.
2. A lokacin ne yaro yake samun zama na gari ko na banza, me amfanar da al'umma ko me cutar da su.
3. Yaro ya fi tasirantuwa da abokansa ko kawayenta fiye da malamansa ko mahaifansa.
4. Yaro yana jin shima daidai yake da kowa a duniya, kuma zai iya yin komai kamar yadda kowa yake yi, haka ita ma yarinyar.
5. A lokacin ne yaro yake neman 'yanci daga ikon mahaipan sa akansa. Yana son dakinsa daban, wajen kwanciar sa da ban, abinci, kayan sakawa da aski sai wanda ransa yake so.
6. A lokacin ne yake jin karfinsa ya kawo, kuma zai iya ja da kowa.
7. A lokacin yaro komai yana yin sa ne gaga-gaga, ba kan gado babu nutsuwa, kuma ba wanda ya isa ya hana shi (a tinaninsa).
Idan kuma iyaye ba su bi hanyar da ta dace ba, to za su sha wahala da shi/ita.
-------------------------
-------------------------
MAFITA:
1. Iyaye su ja yaronsu a jiki, kuma su yi amfani da hikima wajen yi masa gyara da tarbiyyarsa.
2. Sanya yaro ko yarinya a makarantar da ake karatar da boko da addini, ba daidai bane mu cigaba da kai 'ya'yan mu makarantar da za'a koya musu karatun sanin duniya kadai ba, zuwa Islamiyya bayan La'asar ko makarantar hadda Asabar da Lahadi bai wadatar ba(musamman a wannan zamanin da makarantun boko hade da addini suka yawaita a kusan ko ina),
in kuwa ba haka ba to idan suka girma a hannun yan dunia yan boko zalla zasu zama mana matsala a rayuwar mu da kuma makomarmu.
3. Kar su nuna masa karfi ko iko a karon farko, domin zai iya baudare musu, a karshe ya haifar musu da hawan jini.
4. A kula sosai da su waye abokansa, ko kawayenta. A hada shi da nagari, a raba shi da na banza.
5. A samar masa da aikin yi, wajen nuna masa yadda zai dogara da kansa (koda kuwa dan masu kudi ne shi).
6. A tsara masa ayyukan da zai rinka yi a kullun tun daga safe, rana har zuwa dare, misali; makaranta, bacci, cin abinci, ziyara, nazari da muraja'ar karatun sa, hutu, da sauransu.
7. Iyaye su zama abokan 'yayansu wajen bincikar matsalolin 'yayan, da magance musu ita.
8. Ka da a hana yaro wani abu, face sai a maye masa gurbinsa da wani, idan ba haka ba, to zai yi wanda aka hana shi muni.
9. Kar ayi amfani da karfi, da duka, da tsattsauran hukunci wajen ladabtar da shi, har sai idan abu ya ta'azzara.
10. A rinka tunatar da su ayoyin Alqur'ani da Hadisan Manzo s.a.w. da sukai magana akan biyayyar iyaye da hadarin sa'ba musu.i
11. Sannan a rinka hadawa da addu'ar nema musu shiriya da nagarta a wajen Allah s.w.t a koyaushe.
Allaah Ya shiryar mana da zurriyyar mu bakidaya. ALHAMDULILLAHI
This site was designed with Websites.co.in - Website Builder
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support