.Duk wani mai son cin nasara a rayuwa dole ne ya yi karatu, kodai ya yi na takarda da biro ko kuma ya yi na rayuwa, wanda duk ka ji ya ce "Ba dole sai mutum ya yi karatun boko zai zama wani abu ba" maganarsa haka take, amma wani karatu ne ya zarce zaman duniya? Ai ita duniya gaba dayanta makaranta ce, jami'a ce da take da sassa daban-daban, duk sashin da mutum yake son ya shiga zai samu, da za ka dauki mutane guda biyu; wani ya bi layin boko, wato furamare har zuwa jami'a a qarshe ya sami abin kansa, za ka taras wani ya fara da qaramar sana'a ne, ya bari ya koma wata, ko kuma ya qawata ta, za ka ji ya sha wahala iri kaza kafin ya isa wuri kaza, duk wadannan da kake gani karatu ne bambancin hanya ne kawai.
.
Mu a zamanance muna daukar wanda ake ganin kamar ya dan fi sauqi ne, wato shiga a ji, shi din ma ana qoqarin goge qwaqwalwar yaro ne tun yaranta yadda zai iya hararo abubuwan da za su amfane shi a rayuwa, babban dalilin da ya sa aka qirqiro darussan dake buqatar tunani kenan a azuzuwan yara qanana, akan koyar da yaro a ba shi aiki don ya wasa qwaqwalwarsa wajen nemo irin amsar da ake buqata a rayuwa.
.
Idan za a tura yaro wurin sana'a shi ma karatu zai yi, sai dai wannan ya fi karkata ne ga aiki, wato karatu ne amma a aikace, zai san kayan aikin gaba daya da yadda ake sarrafa su, muna da injiniyoyi irin su kanikawa, kafintoci, maqera da magina, wadannan manya-manyan Injiniyoyi ne amma ba su san haka ba, sabanin wadanda suka je makaranta, sau da yawa za ka taras wadanda suka yi karatun boko ba su kai wadanda suka yi a aikace ba, amma da ka ce Injiniya sun san da su kake yi ba wadancan ba, sun yarda da kansu sosai koda kuwa ba abin a qasa, sai su fara bin hanyoyin da za su cimma burinsu, cikin ikon Allah sai ka ga sun sami biyan buqata a dan qaramin lokaci
This site was designed with Websites.co.in - Website Builder
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support