WHATSAPP MAI ABIN MAMAKI

By WAZIRI AKU
8th January, 2020

.Jinjina ga university of WHATSAPP?,  jami'ar da ke bawa kowa certificate da lasisin wa'azi.


Makarantar da budurwa ke koyawa matan aure dabaran rike miji, makarantar da bazawara mai aure 7 ke sayarwa da matan aure maganin mallake miji.


Makarantar da miji Mai dukan matan shi ke koyawa maza yadda ake Zama da mata.


Inda namijin da bai sauke nauyin iyalansa ba ke fadakarwa Akan kyauttawa iyalai.


Makarantar da kowa monitan kan sa ne.


Makarantar da Wanda bashi da tarbiya ke koyar da darasin tarbiya.


Makarantar da yawancin malamanta Musa a baki fir'una a zuci ne.


Madallah da wannan makaranta ta bata bukatar cin jarabawa bare interview, bata damu da yawan shekaru ko karancin shekarun dalibi ba.


WhatsApp makaranta Mai class daya tilo. A cikin class din mutun zai Hadu da sa'an kakan sa na 7, har ya koyawa sa'an kakan nasa zaman duniya da dabarun yau da kullun. 


Whatsapp✅  Mai abin mamaki.

This site was designed with Websites.co.in - Website Builder

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support