.KADAN DAGA CIKIN KURA KURAN NEMAN AURE A WANNAN ZAMANI DA SAMARI KEYI.
RASHIN NEMAN MAI KYAWUN DABI'AH:- Babban abin da ya kamata ka fi mayar da hankali a kai shi ne, neman mace mai kyawawan dabi’u, wacce za ka iya zama da ita don Allah, wacce za ta kai ka tudun-mun-tsira, ba wacce za ta kama hannunka ku tsunduma cikin wuta ba.
YIN KARYA:- Karya tana daga cikin irin abubuwan da ke zubar da mutuncin mutum wajen wacce zai aura. Ka ga matashi yana yi wa yarinya karya, ai shi mai arziki ne, idan ta aure shi ta huta. Ya rika karbar aron abubuwan duniya don ya rude ta. Wannan shi ne mataki na karshe a rashin Wayewa, da fatar masu irin wannan halin za su fadaka su daina.
ROWA:- Dukkan mace tana son kyauta, ya zamana hannun saurayi a bude yake. Duk da ba a dora sharadin aure kan yin kyautar kudi ba, amma Manzon Allah (saw) ya fadi cewa, “Zuciya tana jawuwa bisa son wanda yake kyautata mata, sannan tana kin wanda ya munana mata”. Kenan ashe kyauta za ta iya taka muhimmiyar rawa a wajen neman aure.
Sau tari wasu mazan sukan gabaci mace, su rika nuna tsanin wayewarsu ta zamani. A ganinsu wannan ne dalilin da zai sa su karbu wajen Mace. Sannan a hakan kuma saboda rashin wayewar tasu, babu abin da za su fi mayar da hankali a kai illah neman wacce wai take da wayewar Zamani.
JAHILCI:- Jahilci na daga cikin abin da ke sawa ka samu matsala da wadda kake nema, musamman ma idan ta gano kai jahili ne,to ai ka gama yawo! Don Mace na son namiji mai ilmi duka biyu,wannan zai sa ta soka.
KAZANTA:- Tana daga cikin abubuwan dake sa ka rasa kima a wajen Mace saboda gaskiya mata na da tsabta yadda ya kamata, saboda haka ba sa son namiji kazami. Abin alfaharin Mace ne ta nuna ka a gaban kawayenta ka yi wanka mai kyau, ka hadu!
SHISHSHIGI:- yana dai daga cikin kuskuren da maza ke tafkawa wajen matar da zaI aura. Ka ga namiji ya fiye tambayoyi ko kan halin gidansu , mahaifiyarta mahaifinta, ko ya dinga yi mata tambayoyin da ba su zama dole ba. Lallai wannan na saka ka rasa kimarka wajen macen da za ka aura. Binciken halayen gidan su ba laifi bane, amma tsananta binciken ne laifi. Domin duk wanda aka tsananta masa bincike to ba zaiyi wahala yatsira ko kuwa a lahira ne.
Wadannan kurakuren na taka muhimmiyar rawa wajen zaben aboki ko
abokiyar zama. Da fatan za mu amfana.
08155991156,09064777229
This site was designed with Websites.co.in - Website Builder
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support