FALASAFAR H.ALFINDIKI

By WAZIRI AKU
5th January, 2020


ZAMAN SUNUSI LAMIDO SUNUSI NA BIYU A MATSAYIN SARKIN CIKIN GARI BA KARAMIN BALA'I BANE.

CIKAKKEN NAZARI AKAN SUNUSI LAMIDO SUNUSI

Gaskiya ya kamata mutane su san irin zaben tumun dare da aka yiwa mutanen Kano.

Tun fil azal tsari da tarbiyar rayuwar SLS bata sarauta bace. 
Tafi dacewa da halayarsa lokacin yana dan gaba gaba na Kungiyar Yan uwa Musulmai wadda ake kira Muslim Brotherhood karkashin jagoranchin El Zazzaky(Mutumin Zaria)

Mai hali baya chanja halinsa. Shi yasa Bahaushe yace HALI ZANEN DUTSE.
Yadda duk kayi da SLS yana nan a yadda Sheik Albany da Sheik Jafar(Allah ya rahamta musu) suka bayyana shi.
Sulhu dashi bata lokacine.

Yanzu yana nan yana yiwa Turawa aikin campaign na hana haihuwa ko kayyade iyali a Kano tunda ya yarda Kanawa sunfi kowa talauchi kano itace cibiyar talauci a Nigeria kuma yawan haihuwarsu shike kawo musu talauchi amma fa a tashi fahimtar.

Mai karatu wani abun haushi abun takaici dashi da abokansa sun kasa kafa manya kamfanoni da zasu samarwa da matasa aikin yi kuma su bunkasa arzikin Kano sai tara yara da mata ana basu taliya kwaya daya tan ana daukar hoton video ana turawa Turawa ya zama hujjar talauchi.

Gaskiya barna da zagwan kasa da SLS ya keyiwa Kanawa Allah ne kadai zai saka musu kuma zamansa a mukamin Sarki ba karamin balai bane.

Allah ya bawa Baba Ganduje karfi da juriya don yin jahadin tsige SLM bi jahi rasulullaH ?

This site was designed with Websites.co.in - Website Builder

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support