CUTUTTUKAN ZUCIYA

By WAZIRI AKU
1st January, 2020

.Zuciya ta kan yi rashin lafiya, ta kamu da wasu cututtuka, wadanda za su sa ta k’ek’ashe ta bakance ta lalace har ta mutu, babu wani alheri da zai shiga cikinta sai sharri da mungun nufi da kulla gaba da kiyayya wa mutane ba tare da hakki ba.

Allah da yake siffanta munafukai sai ya ce:
في قلوبهم مرض فزادهم الله مرضا

Ma’ana; akwai cuta a cikin zukatansu, sai Allah ya kara musu cutar.

Daga cikin irin wadannan cutuka na zuciya wadanda suke gadar da bata da zaluntar mutane (da baki ko da aiki) da kin gaskiya akwai:
1. Hasada.
2. Jahilci.
3. Girman kai.
4. Son zuciya.
5. Zalunci.
6. Neman daukaka a bayan kasa.

Wadannan siffofi da makamantansu cutuka ne na zuciya wadanda suke kasheta ta mutu murus idan sun hadu a zuciyar bawa. Kuma Allah (swt) ya siffanta Yahudawa da Munafukai da irin wadannan siffofi.

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
إن الإنسان يجب عليه أن يعرف الحق وأن يتبعه، وهذا هو الصراط المستقيم، صراط الذين أنعم الله عليهم من النبيين والصديقين والشهداء والصالحين، غير المغضوب عليهم ولا الضالين، وهذا هو الصراط الذي أمرنا الله أن نسأله هدايتنا إياه في كل صلاة، بل في كل ركعة.
وقد صح عن النبي – صلى الله عليه وسلم – أنه قال: «اليهود مغضوب عليهم والنصارى ضالون».
وذلك أن اليهود عرفوا الحق ولم يتبعوه استكبارا وحسدا وغلوا واتباعا للهوى، وهذا هو الغي، والنصارى ليس لهم علم بما يفعلونه من العبادة والزهد والأخلاق، بل فيهم الجهل والغلو والبدع والشرك جهلا منهم، وهذا هو الضلال، وإن كان كل من الأمتين فيه ضلال وغي، لكن الغي أغلب على اليهود، والضلال أغلب على النصارى.
ولهذا وصف الله اليهود بالكبر والحسد، واتباع الهوى والغي وإرادة العلو في الأرض والفساد. قال تعالى: {أفكلما جاءكم رسول بما لا تهوى أنفسكم استكبرتم ففريقا كذبتم وفريقا تقتلون} ، [سورة البقرة: 87] ، وقال تعالى: {أم يحسدون الناس على ما آتاهم الله من فضله} ، [سورة النساء: 54] ، وقال: {سأصرف عن آياتي الذين يتكبرون في الأرض بغير الحق وإن يروا كل آية لا يؤمنوا بها وإن يروا سبيل الرشد لا يتخذوه سبيلا وإن يروا سبيل الغي يتخذوه سبيلا} ، [سورة الأعراف: 146] ، وقال تعالى: {وقضينا إلى بني إسرائيل في الكتاب لتفسدن في الأرض مرتين ولتعلن علوا كبيرا} ، [سورة الإسراء: 4] .

“Lallai ya wajaba a kan mutum ya san gaskiya kuma ya bita (ya yi aiki da ita), wannan shi ne hanyar Allah madaidaiciya. Hanyar wadanda Allah ya yi musu ni’ima; Annabawa da Siddikai, da Shahidai, da Salihan bayi, ba wadanda Allah ya yi fushi da su ba, ba kuma Jahilai Batattu ba.
Wannar hanya ita ce hanyar da Allah ya umurcemu da rokon shiriya zuwa gareta a wajensa, a cikin kowace Sallah, kai, a cikin kowace raka’a.
Ya inganta daga Annabi (saw) ya ce:
«اليهود مغضوب عليهم والنصارى ضالون»
“Yahudawa an yi fushi das u, Kiristoci kuma Jahilai ne Batattu”.

Hakan ya faru ne saboda su Yahudawa sun san gaskiya amma ba su bita ba (ba su yi aiki da ita ba), saboda GIRMAN KAI da HASADA da WUCE IYAKA da BIN SON RAI. wannan shi ne BATA (a dalilin rashin yin aiki da gaskiya).
Amma su kuma Kiristoci ba su da Ilmi a kan abin da suke aikatawa na Ibada da gudun duniya, da kyawawan halaye, a tare da su akwai JAHILCI da GULUWWI (azarbabi da wuce iyaka) da BIDI’O’I da SHIRKA, duka saboda JAHILCIN da suke da shi. Wannan shi ne BATA (a dalilin Jahilci da rashin ilmi)….
Wannan ya sa Allah ya siffanta Yahudawa da GIRMAN KAI (kin gaskiya da rena mutane), da HASADA da BIN SON ZUCIYA da BATA (a dalilin kin aiki da gaskiya), da NEMAN DAUKAKA A BAYAN KASA da BARNA A BAYAN KASA.
(GIRMAN KAI):
Allah ya ce:
{أفكلما جاءكم رسول بما لا تهوى أنفسكم استكبرتم ففريقا كذبتم وفريقا تقتلون}

“A duk lokacin da Manzo ya zo muku da abin da ya saba ma son zuciyarku sai ku yi girman kai (ku ki karban gaskiyar da ya zo da ita), wasu manzannin ku karyatasu, wasu kuma ku kashesu”.
(HASADA):
Allah y ace:
{أم يحسدون الناس على ما آتاهم الله من فضله}
“Ko kuma suna yin hasada wa mutane ne a kan abin da Allah ya basu na falala”…..

Duba Minhajus Sunna 2/ 11 – 13.

Abin lura:
1. Wajibi ne mu tashi mu nemi ilmin Sharia, mu san gaskiya; abin da Manzon Allah (saw) ya zo mana da shi.
2. Wajibi ne mu yi aiki da gaskiyar.
3. Yahudawa batattu ne, saboda sun san gaskiya amma sai suka k’i yin aiki da ita, saboda haka sai Allah ya yi fushi da su.
4. Kiristoci batattu ne saboda sun jahilci gaskiya, ba su nemi ilmi ba, sai suka bata saboda jahilci.
5. Yahudawa sun bata ne, kuma Allah ya yi fushi da su, saboda akwai cututtuka a cikin zukatansu, sai zuciyar ta mutu ta k’aik’ashe, saboda suna da GIRMAN KAI (kin gaskiya da rena mutane), da HASADA (hasada wa mutane a kan falala da Allah ya yi musu ta Addini da Ilmi), da NEMAN GIRMA DA DAUKAKA A CIKIN MUTANE.
6. Hasada tana haifar da Girman kai (kin gaskiya da rena mutane), kamar yadda Girman kan yake haifar da Hasadar. Shi ya sa galibi duk mai hasada za ka same shi ba ya karban gaskiya a wajen wadanda yake yi musu hasadan, kuma ya renasu, wannan kuwa shi ne Girman kai, kamar yadda Annabi (saw) ya bayyana.
7. Yin hasada wa mutane a kan falala ta Addini da ta Ilmi, ita ce mafi munin hasada, kuma da ita Yahudawa suka yi fice, kamar yadda Allah ya siffantasu.
8. MAGANIN CUTUTTUKAN ZUCIYA:
(a) Karanta Al- Qur’ani mai girma da Tadabburi (lura da hankalta zuwa ga ma’anoninsa).
(b) Kudurta ingantaccen Imani da Allah da Littatafansa da Manzanninsa shi zai sa bawa yana karban gaskiya daga ko’ina.
(b) Cikakken Tawakkali ga Allah, da ingantaccen Imani da Kaddara shi zai sa bawa ya rabu da hasada.
(c) Sanin hakikanin ‘yan’uwantaka ta Muslunci da Imani, shi zai sa bawa ya so ma dan uwansa abin da yake so ma kansa, hakan sai ya yi masa maganin hasadar da yake yi ma ‘yan uwansa bayin Allah.
(d) Sani tare da Imani da cewa; komai na Allah ne, kuma yana ba da falalarsa ce ga wanda yake so a cikin bayinsa, sa’awun falala ce ta Addini da Ilmi ko falala ce ta abin duniya. Wannan yana maganin hasada.
(e) Yin imani da cewa; Allah ne ya halicci bayinsa, sai ya fifita tsakaninsu, wani ya fika, kai kuma kafi wani, wannan babban magani ne na hasada da girman kai.
(f) Sanin cewa; hasadarka ga wani da Allah ya yi masa falala ba za ta canza abin da Allah ya kaddara na daukaka shi a kanka ba, yana daga cikin manyan magunguna na hasada da girman kai.

Da dai sauran magunguna da idan mutum ya bibiyi nassoshin Al- Qur’ani da Sunna da maganganun malamai da tunani na hankali, zai samu wadanda ba za a iya iyakancesu ba.

Allah ya yi mana afuwa ya kubutar da mu, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.

This site was designed with Websites.co.in - Website Builder

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support